KAI TSAYE Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 17/11/2026
Rahoto kai-tsaye Abdullahi Bello Diginza Mintuna 19 da suka wuce Mun kai hari kan na'urorin radar Amurka a Bahrain - Iran Rundunar kare juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan na'urar radar ta rundunar sojin Amurka da ke sansanin Sheikh Issa a ƙasar Bahrain. A cikin wata sanarwa da sashen hulɗa da jama'a na rundunar ya fitar, ta ce an kai harin ne a matsayin martani ga abin da ta bayyana a matsayin ayyukan adawa da Amurka ke gudanarwa a yankin. Kwanaki kaɗan da suka gabata, rundunar IRGC ta ikirarin cewa na'urorinta sun gano tare da sa ido kan dakarun Amurka da ke Bahrain, amma a lokacin rundunar CENTCOM ta Amurka ta musanta iƙirarin. Har yanzu CENTCOM ba ta fitar da wata sanarwa ba kan ikirarin kai harin da IRGC ta yi ba. Mintuna 51 da suka wuce 'Za mu buɗe mashigar Hormuz ne kawai idan Amurka ta cika sharuɗɗa bakwai' Asalin hoton, Getty Images Mai magana da yawun sojojin Iran ya ce ba za a sake buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta amince da sharuɗɗa bakwai da Iran ta gindaya. Ya kuma gargaɗi jiragen ruwa da su guji amfani da hanyoyin da ya ce Amurka na bayyana a matsayin amintattu. Da yake magana a birnin Bandar Abbas, Amir Akraminia ya ce rundunonin sojin Iran suna cikin cikakken shiri, kuma sun karɓe iko da muhimman wurare da ke gabashi da yammacin mashigar Hormuz. Ya ƙara da cewa ba za a sake buɗe wannan muhimmiyar hanyar ruwa ba har sai Amurka ta amince da bukatun Iran. A cewarsa, jiragen ruwa da ke amfani da hanyoyin da Iran ba ta amince da su ba na iya fuskantar haɗarin nakiyoyin da aka dasa a ƙarƙashin tekun da kuma harbe-harbe. Ya ce tsaron jiragen ruwa zai samu ne kawai idan aka haɗa kai da dakarun Iran tare da bin hanyoyin da rundunar soji da kuma rundunar juyin juya halin Iran suka tanada. Mai magana da yawun ya kuma yi gargaɗin yiwuwar sake ɓarkewar rikicin soja, yana mai cewa idan aka sake ɗaukar wani mataki da ya kira kuskure, ko kuma ƙasashen yankin suka bi buƙatun Washington da ya bayyana a matsayin haramtattu, sansanonin da muradun abokan gaba za su fuskanci martani cikin gaggawa da karfi. Sa'a 1 da ta wuce 'Zan tsaya takarar shugaban ƙasa idan mahaifina ya sauka' Asalin hoton, Getty Images Babban kwamandan rundunar tsaron ƙasar Uganda (UPDF), Janar Muhoozi Kainerugaba, ya ce zai tsaya takarar shugaban ƙasar idan mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, ya sauka daga mulki. Ya ce babu wanda zai iya hana shi cimma wannan buri nasa. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, Muhoozi ya ce yana dogaro ne ga Allah da kuma al'ummar Uganda. "Zan tsaya takarar shugaban kasa idan Mzee ya sauka daga mulki. Babu wanda zai hana ni wannan buri. Na ɗora buri ga Allah da kuma ƴan uwana ƴan Uganda," in ji shi. Wannan furuci na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar gwamnati ta National Resistance Movement (NRM) ta musanta rahotannin da ke cewa kwamitinta na ƙoli ya yi watsi da wani kuduri na goyon bayan Muhoozi ya gaji mahaifinsa. Sakataren Janar na jam'iyyar NRM, Richard Todwong, ya ce rahotannin da ke ikirarin an gudanar da wani taron sirri na kwamitin a ranar 10 ga Nuwamba ba su da tushe. Ya ƙara da cewa jam'iyyar za ta sanar da matsayarta a lokacin da ya dace, ta hanyar hanyoyinta na hukuma. Kalaman Muhoozi sun kuma sake tayar da tambayoyi game da yiwuwar sauyin shugabanci a cikin jam'iyyar NRM mai mulki, a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan rawar da yake takawa a siyasar kasar. Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko zai samu isasshen goyon baya a cikin jam'iyyar da zai tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa ba. Sa'a 1 da ta wuce Ba za mu bari yaƙinmu da Iran ya kai shekara biyu ba - Vance Asalin hoton, Reuters Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce gwamnatin Amurka ba za ta bari yaƙin da take yi da Iran ya ɗauki tsawon shekara biyu ba. Ya kuma jaddada cewa shirin nukiliyar Iran na ci gaba da zama barazana ga Amurka. "Mun yi wa al'ummar Amurka alƙawarin cewa ba za mu sake shiga yaƙe-yaƙen da ba su da iyaka ba," in ji Vance a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Fox News ranar Litinin. "Haƙiƙa shugaban ƙasa ya yi imanin cewa dole ne a lalata shirin nukiliyar Iran, kuma gaskiya ne cewa wannan shiri barazana ne ga Amurka. Amma ba za mu bari wannan rikici ya rikiɗe ya zama yaƙin da zai ɗauki shekara 10 ko 15 ba, ko ma shekara biyu," in ji shi. Kalaman Vance na nuni ne ga shekaru biyun da suka rage wa wa'adin mulki na biyu na Trump. Sa'o'i 2 da suka wuce Iran ta ce ta kama jirgin Amurka maras matuƙi Asalin hoton, Getty Images Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce dakarunta sun yi kutse cikin tsarin sarrafa jirgin yaƙin Amurka maras matuƙi, ƙirar MQM-10, sannan suka saukar da shi tare da ƙwace shi. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da safiyar Talata, ta ce an "karbe ikon jirgin ne a sararin samaniyar kudancin tsibirin Qeshm, kafin daga bisani a saukar da shi lafiya". IRGC ta ce ta yi hakan ne yayin wani samamen yaƙi ta hanyar na'urorin laturoni (electronic warfare) da ƙwararrun rundunar sojin saman IRGC suka gudanar cikin kwarewa da nasara. Har yanzu rundunar sojin Amukra da ke Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ba ta mayar da martani kan ikirarin Iran ɗin ba. Sa'o'i 2 da suka wuce An kai munanan hare-hare Ukraine cikin dare Magajin garin Kyiv, Vitaliy Klitschko, ya ce wasu makamai masu linzami da aka harba sun afka wa gadoji biyu da ke kan kogin Dnipro a babban birnin Ukraine. Jami'an birnin sun kuma bayyana cewa harin ya shafi layin dogo na ƙarƙashin ƙasa , lamarin da ya sa aka dakatar da zirga-zirga a wani ɓangare na layin na ɗan lokaci. Wakilin BBC da ke Kyiv ya ce ya ji ƙarar fashewar wasu abubuwa da daddare, yayin da aka ba da rahoton wani sabon jerin hare-hare da sanyin safiyar yau. Rundunar sojin saman Ukraine ta ce an harba makamai masu linzami masu sarrafa kansu zuwa Kyiv daga cikin yankin Rasha. Wakiliyar BBC ta ce a wani labarin kuma, shugaban da Rasha ta naɗa a yankin Crimea da take iko da shi ya ce Ukraine ta sake kai hari kan gadar Kerch, wadda ke haɗa yankin da Rasha, a dare na biyu a jere. Sa'o'i 3 da suka wuce Assalamu alaikum Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata. Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku halin da duniya ke ciki. Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin bayyana mana ra'ayoyinku kan labaran da muke wallafawa